Jagoran jam’iyyar APC na kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya soke taron tattaunawa da wasu jiga-jigai kan harin da ‘yan ta’adda suka kai kan wani jirgin kasa da ya taso daga Abuja zuwa Kaduna ranar Litinin.
Dama dai An shirya taron ne a ranar Talata a Legas domin tunawa da cikar Tinubu shekaru 70 da haihuwa.
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC ya bukaci malamai da duk wanda ya gayyata halartar taron da su yi addu’ar Allah ya taimaki Najeriya ta samu nasarar yaki da ta’addanci.
Ya ce a matsayinsa na babban dan kasa ba zai iya yin bikin ba yayin da wasu ke cikin bakin ciki. Ya ce kowa ya koma gida a yi wa Nijeriya addu’a.
Tinubu ya Kuma yi nuni da cewa, ya kamata a yi bikin zagayowar ranar haihuwarsa cikin tunani da kuma yi wa kasa addu’a.
Inda kuma ya ce, “Bai kamata a yi wannan taron ba. na soke wannan maganar Taron, saboda abin da ya faru a Kaduna. Ina kira gare ku da ku yi addu’ar Allah Ya sa Najeriya ta ci nasara a wannan yaki da masu aikata muggan laifuka.”
Comments 1