Jami’an Hukumar Yaki da Yiwa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) na ci da sabbata juyata da Daraktan Kudi kuma Akanta na Hukumar Raya Yankjn Neja Delta (NDDC), Mista Eno Ubi Otu.
Daily Trust ta ruwaito cewa jami’an hukumar yaki da cin hanci da rashawa sun kama Otu ne da misalin karfe 11:15 na safe dangane da zargin karkatar da kudaden haraji da suka kai sama da Naira biliyan 25.
Wata majiya daga Hukumar ta shaida wa majiyar Dimokuradiyya cewa har yanzu jami’in NDDC na tare da jami’an hukumar EFCC da misalin karfe 7:15 na yamma lokacin da aka hada wannan rahoto.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kotu Ta Tsare Wani Mutum Bisa Yiwa Wata Yarinya Fyade
A cewar jami’in, kama Otu ya kasance wani babban bincike na rahoton binciken kwakwaf kan hukumar NDDC.
Sai dai duk Kokarin jin ta bakin mai magana da yawun Hukumar ta EFCC Wilson Uwujaren abun ya ci tura, yayin da kiran wayarsa bbai dauka ba.