By Abbas Yakubu Yaura
Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya (NCAA) ta rufe cibiyar kamfanin Globacom (Glo) dake Wuse 2 Abuja kan bashin da ake binsa na naira biliyan 4.7bn.
An dai gudanar da atisayen ne karkashin jagorancin Darakta Janar na NCAA, Kyaftin Musa Nuhu, kuma Ministan Sufurin Jiragen Sama, Senata, Hadi Sirika ne ya kula da lamarin.
Darakta Janar din yace za a ci gaba da rufewar ne a wasu cibiyoyin kamfanin Glo’s na (MSC) dake fadin kasar har sai kamfanin sadarwa ya yi alkawarin biyan kudi.