Hukumar gudanarwar Gasar Firimiyar Kasar Ingila ta fitar da wata sanarwar dake bada tabbacin cigaba da buga wasannin mako na 8 a karshen makonnan.
Daily Post ta ruwiato cewa, Sai dai uku daga cikin wadannan wasanni an dakatar da buga su.
KARANTA WANNAN LABARIN: An Hana Gidajen Talabijin Din Kenya Yada Shirin Rantsar Da Ruto
An dai dage wasannnin ne domin girnama mutuwar Sarauniyar Ingila ta biyu wato Elizabeth.
Jadawalin wasannin da za a fafata a karshwn makonnan su ne:
Ranar Juma’a 16 ga watan Satumba
20:00 Aston Villa Da Southampton (Sky Sports)
20:00 Nott’ham Forest Da Fulham
Ranar Asabar 17 Ga watan Satumba
12:30 Wolves Da Man City (BT Sport)
15:00 Newcastle Da AFC Bournemouth
17:30 Spurs Da Leicester City (Sky Sports)
Wasan da aka dakatar— Brighton Da Crystal Palace
Ranar Lahadi 18 Ga watan Satumba
12:00 Brentford Da Arsenal (Sky Sports)
14:15 Everton Da West Ham (Sky Sports)
Wasan da aka dakatar—Chelsea v Liverpool
Wasan da aka dakatar— Man Utd v Leeds
A WANI LABARIN KUMA: Zaben 2023: Tikitin Musulmi-Musulmi Tsan-Tsan Yaudara Ne— Sheikh Ahmad Gumi
Fitaccen malamin addinin musuluncin nan, Sheikh Ahmad Gumi ya bayyana tikitin tsayawa takarar musulmi da musulmi a matsayin yaudara, yana mai cewa abin da Najeriya ke bukata a 2023 gogaggen shugaba ne da zai iya hada kan al’umma.
Ya ce Najeriya ba ta bukatar karamin dan siyasa a matsayin shugaban kasa, sai dai gogaggen dan siyasa da zai jagoranci ta a zaben 2023 mai zuwa.