Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya Usman Baba ya amince da karin girma ga kananan jami’ai 21,039.
Wannan nazuwa ne bayan jami’an sun kwashe tsawon Lokaci Batare da samun Karin Girma Wanda run shekarar 2017.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar, CSP Muyiwa Adejobi ne ya sanar da amincewar a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis.
Karin Girman ya ƙunshi jami’an dake mukamin sajen 20,572 zuwa Sufeto, sai Kofur guda 324 da aka Mai da su zuwa Sajan, da Sabbin yan sanda Masu mukamin kostabul guda 143 zuwa Kofur.
Adejobi ya ce wani bangare ne na kokarin inganta jin dadin jama’an, yanayin hidima da kara kwarin gwiwar ma’aikatan domin samun inganci.
Baba ya tabbatar da cewa zai ci gaba da jajircewa wajen ganin an samar wa jami’an jindadi da walwalar, domin ganin an baiwa ma’aikatan da suka cancanta tukuicin don karfafa kwazon aikin su.
IGP ya sanar da manyan jami’an ‘yan sanda cewa hukumar kula da harkokin ‘yan sanda ta kasa (PSC) za ta saki Takaddun karin girma da aka yi musu, Nan bada jimawa ba..
Ya yaba wa sabbin jami’an da aka kara wa girma bisa jajircewar da suka nuna, ya kuma hori su da su girmama sabbin mukaman da aka ba su a matsayin wani kira na sabunta himma da kwazo da kishin kasa a lokacin da suke bakin aiki.