Sa’o’i kadan bayan jam’iyyar adawa ta NNPP, ta yi kira da a sauya kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, Mamman Dauda, bisa zargin nuna son kai, babban sufeton ‘yan sanda Alkali Baba, ya bayar da umarnin sauya masa wajen aiki zuwa jihar Filato domin gudanar da zabe. Daily Nigerian ta rawaito
A ranar Lahadin da ta gabata ne jam’iyyar NNPP ta yi barazanar fara zanga-zanga a fadin kananan hukumomi 44 na jihar Kano domin nuna adawa da kamawa da tsare wasu manyan mambobinta sama da 100.
KU KARANTA: Gwamna Zulum Ya Baiwa Masu Sana’ar Dinki 5,340 Tallafin Naira Miliyan N100m
Jam’iyyar ta ce muddin ba a cire kwamishinan yan sandan ba, aka kuma hukunta shi kan rashin da’a da ya yi, za su ci gaba da zanga-zangar.
Da yake jawabi a madadin jam’iyyar NNPP a Kano ranar Lahadi, dan takarar Sanatan Kano ta Arewa a majalisar dattawa, Baffa Bichi, ya yi zargin cewa kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mamman Dauda, na hada baki da jam’iyyar APC mai mulki domin murkushe jam’iyyar wasu jam’iyyun wajen fifita APC.
Sai dai a wata sanarwa da DAILY NIGERIAN ta samu, IGP din ya sauya Mista Dauda zuwa Filato sannan ya tura CP Mohammed Yakubu Kano.
Jaridar DAILY NIGERIAN ta ruwaito cewa, IGP din ya kuma tura manyan jami’an ‘yan sanda zuwa kowane gundumomi 109 na ‘yan majalisar dattawan kasar nan a lokacin zabe.
A wani sabon sako da aka fitar bayan soke na baya ba zato ba tsammani, IGP ya tura CP Ita Uku-Udom zuwa gundumar Kano ta tsakiya; sai kuma CP Sunday Babaji zuwa gundumar Kano ta Kudu, da DCP Abaniwonda Olufemi zuwa Kano da Arewa.
DIMOKURAƊIYYA ta rawaito cewa yanzu haka yanayin siyasar jihar Kano na kara daukar dumi, tsakanin APC da kuma NNPP.
A wani labarin kuma: Dan Takarar Gwamnan Na NNPP Ya Yi Alkawarin Sabunta Birane Idan Aka Zabe Shi
Farfesa Oba Abdulraheem, dan takarar gwamnan jihar NNPP na jihar Kwara, ya ce zai fara aikin sabunta birane da ababen more rayuwa, idan aka zabe shi a matsayin gwamnan jihar.
Da yake magana kan ajandarsa ga al’ummar jihar Kwara a wata hira da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, Oba ya ce zai fara aikin gyara da kuma kula da manyan titunan birane da na karkara.