Sunan shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan baya cikin jerin sunayen ‘yan takara na karshe da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta wallafa.
Daily Trust ta ruwaito cewa, An dade ana takun saka tsakanin Lawan da Bashir Machina kan tikitin jam’iyya mai mulki a Yobe ta Arewa da Lawan ke wakilta a halin yanzu.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ku Kula Da Alakar Da Kuke Kullawa Da Rasha– Shugaban Poland Ya Gargadi Kasashen Afrika
Sai dai, Godswill Akpabio, tsohon ministan harkokin Neja Delta ne ya shiga cikin jerin sunayen.
A farkon makon nan ne wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta umurci INEC da ta amince da wallafa sunan Akpabio a matsayin dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na gundumar Akwa Ibom ta Arewa maso Yamma a zaben shwkarar 2023 mai zuwa.
A WANI LABARIN KUMA: An Tsare Wani Matashi A Gidan Yari, Bisa Daba wa Mahaifiyarsa Wuka A Fuska
An tsare wani matashi a jihar Adamawa bisa zarginsa da daba wa mahaifiyarsa wuka a zazzafar takaddama da ta barke a tsakaninau.
Ibrahim Umar mai shekaru 22 a karamar hukumar Michika da ke arewacin Adamawa an tsare shi a gidan yari bayan da ya amince ya daba wa mahaifiyarsa, Hajiya Lami Mallum wuka, a yayin wata takaddama da ta barke.