Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta sanya ranar gudanar da zaben cike gurbi na Yan Majalissun tarayya, na jiha da kuma Gwamnoni a wasu jihohin.
INEC ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin a shafinta na Facebook.
KARANTA WANNAN LABARIN: Mahaifin Obasanjo Ba Cikakken Bayerabe Bane, Watakila Dan Kabilar Igbo Ne – Fani-Kayode
INEC ta ce za a gudanar da dukkanin zabukan cike gurbin ne a ranaar 15 ga watan Afurilun shekarar 2023.
Sai dai INEC ba ta yi cikakken bayani ba kan gudanar da zaben, inda kuma ta ce, za ta yi karin haske nan ba da jima wa ba.
Idan ba amanta ba, Jami’an tattara sakamakon zabe a jihohin Kebbi da Adamawa da dai sauransu sun bayyana zabukan Gwamnonin jihar a matsayin wadanda ba su kammalu ba.
Kana a zaben da aka gudanar na ranar 25 ga watan Maris din shekarar nan, Jami’in tattara sakamakon zabe dake yankin Kebbi ta Arewa ya bayyana zaben dan majalissar Dattijan yankin a matsayin wanda bai kammalu ba.
A wani labarin kuma, Mahaifin Obasanjo Ba Cikakken Bayerabe Bane, Watakila Dan Kabilar Igbo Ne – Fani-Kayode
Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode ya bayyana ra’ayin cewa mahaifin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ba dan kabilar Yarbawa bane.
Fani-Kayode ya ce ‘shirun’ da Obasanjo ya yi kan wani kalami da dan kasuwar nan dan kabilar Ibo, Emmanuel Iwuanyanwu ya yi a baya-bayan nan cewa Yarabawa ‘yan iskan ‘yan siyasa ne, hakan ya nuna cewa mahaifin tsohon shugaban kasar dan kabilar Ibo ne, ba Bayerabe ba