• IPOB ta yi barazanar tsayar da al’amuran cak a yankin Kudu maso Gabas.
• Ta ce wannan daya ne daga cikin matakan da zata dauka na tabbatar da an saki Kanu cikin Koshin Lafiya.
• Barazanar na zuwa ne kwanaki kadan bayan Wasu da ake zargin yan kungiyar ne, sun kashe wani jami’in dan sanda a Mai mukamin DPO.
Kungiyar dake fafutukar kafa kasar Biafra IPOB, ta yi barazanar tsayar da al’amurori cak, na tsawon sati guda a yankin gudu masu Gabashin kasar nan, biyo bayan ci gaba da tsare jagoran kungiyar Nnamdi Kanu.
Jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito yadda Kanu ya tsare kasar nan, bayan belin din shi, da Kotu ta bayar a shekarar 2017. Inda aka sake kama shi a kasar waje, kuma a ka dawo da shi kasa Nigeria.
Haryanzu dai ya na tsare ne a hannun hukumar tsaro ta farin kaya ta kasa wato DSS.
A cikin wata sanar wa da ya sanya wa hannu, daya daga cikin jiga-jigan kungiyar Mai suna Chika Edozie ya bayyana cewa, Gwamnatin tarayya na da kwanaki gona sha daya kacal da su saki Kanu, domin kauce wa dakatar da al’amuran.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan bindiga sun saki Basaraken Kaduna da su ka yi garkuwa da shi
“Umarnin da Kungiyar ta bayar, na bukatar gaggawar sakin Mazi Nnamdi Kanu, kafin nan da ranar 8 gawatar Ogustan shekarar 2021, saba wa wannan umarnin kuwa, zai sa a dakatar da dukkannin al’amurori a yankin Biafran, daga ranar 9 ga watan Ogustan shekarar 2021” Kamar yadda sanarwar ta bayyana.
“Don kawar da wata tantama na wannan dakatar da al’amuran na yankin Biafra, zai kun shi kowa ce ranar Litinin, har sai an saki jagoran kungiyar, batare da wata yarjejeniyar ba”
“Wannan kullen na tsawon mako guda, na daya daga cikin matakai da za mu dauka, domin tabbatar da sakin jagoran na mu, cikin koshin lafiya” inji sanarwar.
Edonzie na wannan barazanar ce, kwanaki biyu kachal, bayan wasu da ake zargin mayakan kungiyar ce ta IPOB, sun kashe wani jami’in dan sanda Mai mukamin DPO, a wani musayan wuta da su kayi da jami’an yan sanda, a mahaifar Gwamnan Hope Uzodima na jihar Imo.