A yanzu haka akwai dimbin jama’a a ofishin babban bankin Najeriya (CBN) da ke Marina a Legas. Kamar yadda Daily Trust ta ruwiato.
Dandazon ya kunshi mutanen da ke kokarin musanya tsofaffin kudade bisa umarnin shugaban kasa Muhammadu Buhari.
KARANTA WANNAN LABARIN: Zabe: Kada Ku Goyi Bayan ‘Yan Takara Marasa Takaddun Shaidar Karatu – Kwankwaso Ga Dalibai
A jawabinsa da yayi wa yan kasa a ranar Laraba, Buhari ya bayyana cewa tsofaffin takardun kudi na N500 da N1000 sun sun tashi aiki bisa doka, inda ya umurci ‘yan Najeriya da su kai takardun kudin su zuwa CBN da wuraren da aka kebe.
Ya kuma umurci CBN da ta sake sakin tsofaffin takardun kudi na N200 har zuwa ranar 10 ga Afrilu.
A dai cigaba da sukar lamarin, biyo bayan kalaman Buhari, musamman daga wasu gwamnonin jam’iyyar APC mai mulki.
Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya ce tsohon takardun kudi na N500 da N1000 a jihar za’a iya ci gaba da amfani da su, har sai kotun koli ta yanke hukunci.
A halin da ake ciki dai jami’ai na kokawa kan yadda jama’a ke taruwa a ofishin CBN na Legas. A lokaci guda, sun nemi masu ajiya da su kai tsofaffin takardun zuwa bankunan kasuwancin su, amma jama’a sun ƙi.
Da yake tsokaci kan lamarin, wani mai amfani da kafafen sada zumunta mai suna Malik ya ce dan uwansa ya isa babban bankin kasar CBN a Marina da misalin karfe 6 na safe kuma shi ne na 420 a cikin jerin gwanon mutanen.
A wani labarin kuma, 2023: Miyagun Mutane Suna Amfani Da Buhari Wajen Durkusar Da APC – El-Rufai
Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kyale wasu mutane da ya bayyana a matsayin “mugayen mutane” su yi amfani da shi wajen yakar jam’iyyar siyasar da ta ba shi dama don bauta wa Najeriya.
Ya ce mutanen da ke amfani da shugaban kasa a matsayin makamin kayar da jam’iyyar APC na yin hakan ne saboda sun kasa yin yunkurin tilasta wa nasu dan takarar a jam’iyyar a zaben fidda gwani na watan Yuni shekarar 2022.