Daga: Uzairu Lawal Rigasa
Jami’an hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) sun kai farmaki gidan wani mai tattaunawa da yan ta’addan da aka kama, Tukur Mamu a Kaduna da sanyin safiyar yau Alhamis. Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
‘Yan sandan sun zo ne a cikin motoci kusan 20 a wani abin da wani shaida ya bayyana.
KARANTA WANNAN LABARIN: Tinubu, Atiku, Obi, Da Sauransu Zasu Biya Naira Milliyan 10 Kafin Lika Fastocinsu A Jihar Kogi
“Sun far wa gidan tare da kwashe takardu, wayoyi da kwamfutoci. An umurci wadanda ke cikin gidan da su sanya hannu a kan takardar da ba su karanta ba kafin jami’an su mayar da ita,” inji shaidan.
Daily Trust ta cewa bayan sun kai farmaki a gidansa, sun kuma je ofishin sa da ke Kaduna.
Wasu daga cikin Wadanda aka ceto wadanda harin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna ya rutsa da su na ofishin Mamu kafin su sake haduwa da iyalansu.
Majiyoyin tsaro sun ce an kama Mamu ne bisa zarginsa da hannu wajen karbar kudin fansa da kuma kai makamancin haka ga ‘yan ta’adda domin musanya wadanda aka yi garkuwa da su.
Dimokuradiyya ta ruwaito yadda aka kama Mamu a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano da ke Kano a ranar Laraba da rana.
Mawallafin mazaunin Kaduna wanda aka fara kama shi a Masar an tsare shi tsawon sa’o’i 24 kafin a dawo da shi Najeriya.
A Wani Labarin Kuma, Hajj 2022; Gwamnan Zamfara Ya Bada Umarnin Maidowa Alhazan Jihar Naira 50,000
Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya amince da mayar da Naira 50,000 ga kowane mutum 1,318 a jihar da suka yi aikin Hajjin shekarar 2022.
Daily Trust ta ruwaito cewa, Kwamishinan yada labarai Malam Ibrahim Dosara ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Gusau ranar Laraba.