Jam’iyyar PDP a cikin wata sanarwa da sakataren yada labaranta na kasa, Debo Ologunagba ya fitar ta bayyana cewa ranar karshe ta dawo da fom din da aka riga aka siya, an sake tsawaitawa sabanin na baya.
A cewar jam’iyyar, ranar ƙarshe na mika fom ɗin da aka riga aka kammala siya na Yan takarar Majalisar Dokoki na Jiha : ita ce Lahadi, 10 ga Afrilun shekarar 2022, da ƙarfe 6 na yamma.
Yayin da ake shirin tantance ‘yan takarar majalisun dokoki na Jiha da kuma na kasa a ranakun Talata, 12 ga Afrilu shekarar shekarar 2022, da Alhamis, 14 ga Afrilu, 2022.
A wani bangare sanarwar ta yi nuna da cewa “Duk sauran ranakun sun kasance kamar yadda aka tsarasu tun farko.
“Don guje wa shakku, ranar ƙarshe don siyan duk fom ɗin yanzu an tsawaita shi har zuwa ranar Juma’a, 8 ga watan Afrilu shekarar 2022.”