Rahotanni daga jihar Texas a kasar Amurka sun ce wani jirgin sama dauke da fasinjoji 21 ya rikito a yau Talata.
Sai dai dukkanin mutanen da hatsarin ya rutsa da su sun tsallake rijiya da baya, domin kuwa babu wanda ya rasa ransa.
Babu wani karin bayani ya zuwa hada rahoton nan.