Daga: Abbas Yakubu Yaura
Kamfanin jiragen sama na Azman ya dakatar da ayyukan sa saboda gazawar kamfanin wajen sabunta satifiket dinsa na ayyuka AOC, kamar yadda Daily Trust ta tattaro.
An ce Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya NCAA ta dakatar da Azman ne saboda gaza cika sharuddan sabunta AOC.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamna Fayemi Ya Bada Umarnin Gyara Hanyar Ekiti Cikin Gaggawa
An kuma gano cewa hukumar ta ba ta lokaci mai tsawo don sabunta AOC, amma ta gaza duk da cewa ta ba kamfanin jirgin wasu wa’adin kwanaki 30 don biyan bukatun.
Sai dai wata majiya a kamfanin jirgin ta ce an biya kudin da ake bukata kuma watakila yau an warware matsalar.
Majiyar ta ce kamfanin jirgin zai bayar da cikakken bayani a wata ranar nan gaba.
A wani labarin kuma, Da Dumi-Dumi: Mahaifiyar Gwamnan Jam’iyyar APC Ta Rasu
Mahaifiyar gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, Lady Evangelist, Grace Akeredolu ta rasu.
Kafin rasuwar ta dai ta yi bikin cikarta shekaru 90 a Duniya a watan Fabrairun da ya gabata.