Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Najeriya (AON) ta sanar da dakatar da ayyukanta, daga ranar litinin, sakamakon tashin gwauron zabin da ake samu na farashin man jiragen sama, wanda ya kai Naira 700 a kowacce lita.
Masu gudanar da aikin sun tausayawa fasinjojin, inda suka ce halin da ake ciki yanzu da man Jet A1 ya sa kudin gudanar da ayyuka ya kai zuwa sama da kashi 95 cikin dari.
Ma’aikatan sun bayyana hakan ne a wata takarda da shugabanta Alhaji Abdulmunaf Yunusa Sarina ya aikewa ministan sufurin jiragen sama, Sanata Hadi Sirika.
Matakin Sarina ya sami amincewa daga manyan shugabannin duk kamfanonin jiragen sama na cikin gida.
Wasikar ta kara da cewa: “Cikin nauyi da kishin kasa ne kungiyar ma’aikatan kamfanin jiragen sama na Najeriya (AON) suka ci gaba da turawa tare da ba da tallafin ayyukansu ga jama’armu masu daraja ta Najeriya a cikin watanni hudu da suka gabata duk da ci gaba da hau-hawar farashin man JetA1 da sauran farashin aikin kayayyakin aikin mu”.
“A kan kari, farashin man jirgin (JetA1) ya tashi daga Naira 190 kan kowace lita zuwa Naira 700 a halin yanzu. Babu wani kamfanin jirgin sama a duniya da zai iya jure wannan gigicewa kwatsam daga irin wannan tashin hankalin a cikin kankanin lokaci Wanda Hakan yasa muka dauki wannan Mataki”.
A wani labarin Kuma na daban.
Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, a ranar Juma’a, ya bayyana babban kalubalen da jam’iyyar APC ta haddasa a Najeriya.
Atiku ya ce jam’iyyar APC ta jawo wa Najeriya rarrabuwar kawuna ne kawai.
Tsohon Mataimakin Shugaban kasar ya koka da yadda Najeriya ta fi rabuwa a karkashin gwamnatin APC fiye da lokacin yakin basasa.
Atiku ya yi wannan maganar ne a Legas a taron ‘ya’yan jam’iyyar PDP gabanin gudanar da zaben fidda gwani da za a yi.
A cewar Atiku: “Muna raye kan kalubalen da jam’iyyar APC ta jawo mana a kasar nan.
“Babban kalubalen da jam’iyyar APC ta kawo shi ne rashin hadin kai. Ba a raba mu haka a baya ko a lokacin yakin ba.
“Muna da alhakin korar jam’iyyar amma dole ne mu hada kanmu domin mu iya yin hakan, jam’iyyar PDP ta Legas ta rabu shekaru da dama, ina kira ga PDP ta Legas da ta kawo hadin kai a jam’iyyar, ina kira ga manya. don Allah a tabbatar da hadin kai a jam’iyyar reshen jihar Legas domin mu karbi ragamar mulkin jihar.
“Ina fatan yin aiki tare da ku don mayar da PDP jihar Legas. Ba ma son Legas ta kasance ƙarƙashin iyali ɗaya. Muna son Legas ta zama ta ’yan Legas.
Kazalika ya kamata mu guji yin irin kuskuren da muka yi tsawon shekaru. Zan ci gaba da yin aiki tare da ku har sai mun cimma nasara.”