Kanin tsohon Gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, Kwamared Inuwa Musa, ya rasu.
Bayanin hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Shugaban Kwankwasiyya Media Center Sanusi Bature Dawakin Tofa.
Sanarwar ta ci gaba da cewa “tare da mika wuya ga ikon Allah baki daya, muna sanar da rasuwar Kwamared Inuwa Musa Kwankwaso, kanin tsohon gwamnan jihar Kano Sen. Engr. (Dr.) Rabiu Musa Kwankwaso.”
Ya rasu yana da shekaru 64 a safiyar ranar Litinin 20 ga Disamba, 2021 a asibitin koyarwa na Aminu Kano bayan ya sha fama da jinya.
Marigayin ma’aikacin gwamnati mai ritaya ne kuma injiniyan noma wanda ya samu horo a Ibadan da Amurka.
Ya yi aiki a wani sashi na hukumar gandun daji a Kano tsawon shekaru.
Inuwa ya rasu ya bar mata da ’ya’ya mata biyu – Barr. Nafisa Inuwa da Zainab Inuwa – da ‘yan uwa da dama.
An yi jana’izar marigayin kamar yadda addinin Musulunci ya tanada a gidan iyalansa da ke kauyen Kwankwaso a karamar hukumar Madobi