Wani ginin beni ya ruguje a kan titin Sonuga, Palm Avenue, a unguwar Mushin dake jihar Legas.
Babban Sakatare na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Legas, Dakta Olufemi Oke-Osanyinyolu, ya tabbatar wa da wakilinmu faruwar lamarin a ranar Juma’a.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ina Kalubalantar PDP Da Ta Dakatar Da Ni Daga Jam’iyyar – Wike
Ya ce, “Wani ginin beni ya ruguje a Mushin ‘yan mintoci da suka wuce. Ana ci gaba da aikin ceto.”
Har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto, ba a iya tabbatar da cewa wani ya makale a cikin baraguzan ginin da ya ruguje ba.
A wani labarin kuma, ASUU Za Ta Daukaka Kara A Yau – Falana
A ranar Juma’a ne kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) za ta shigar da kara a gaban kotun daukaka kara da ke Abuja, domin ta ba da umarnin shiga tsakani tare da yin watsi da hukuncin da kotun masana’antu ta kasa ta yanke na janye yajin aiki da take da kuma Mambobin ta su koma bakin aiki.
Lauyan kungiyar ASUU kuma mai fafutukar kare hakkin bil’adama, Mista Femi Falana, ya tabbatar da hakan a ranar Alhamis ga jaridar Tribune Online a wata tattaunawa da suka yi da ita.