By Abbas Yakubu Yaura
Masarautar Saudiyya ta sanar da cewa maniyyata miliyan daya ne za su yi aikin Hajjin bana na wannan shekara.
Masarautar a cikin wani sako da ta wallafa a shafinta na twitter ta hannun hukuma ma’aikatar Hajji da Umrah ta ce adadin zai kasance na alhazan kasashen waje da na cikin gida.
Idan za a iya tunawa, an hana alhazan kasashen waje zuwa aikin hajji na tsawon shekaru biyu bayan barkewar annobar cutar COVID-19 a shekarar 2020, inda ‘yan kasar Saudiyya 60,000 ne kawai aka ba su izinin zuwa aikin hajjin shekarar 2021.
A kololuwarta, kasar na daukar mahajjata miliyan biyu a duk fadin duniya domin gudanar da aikin hajji.
A cikin sanarwar, ta ce Masarautar Saudiyya na neman kiyaye nasarar da ta samu wajen shawo kan cutar ta Covid-19.
Don haka za a ba wa ‘yan kasa da shekaru 65 damar gudanar da aikin hajji tare da yin aikin hajji na sa’o’i 72 da kuma gudanar da gwajin PCR.
“Yawancin maniyyatan da suka fito daga wasu kasashe na musamman don aikin Hajjin bana za su kasance ne bisa ka’idojin da aka ware wa kowace kasa da kuma la’akari da bin duk wasu shawarwarin lafiya.
“Ma’aikatar Hajji da Umrah ta sanar da cewa za a gudanar da aikin Hajjin bana ne bisa ga ka’idoji kamar haka: Hajjin bana a bude yake ga wadanda ba su kai shekara 65 ba, kuma sun samu babban rigakafin Covid-19 da ma’aikatar lafiya ta Saudiyya ta amince da su.
“An bukaci alhazai da ke fitowa daga wajen Masarautar da su gabatar da sakamakon gwajin Covid-19 PCR daga gwajin da aka yi a cikin sa’o’i 72 na lokacin da za a tashi zuwa Masarautar.
Kazalika Ma’aikatar Hajji da Umrah ta ba da umarnin cewa dukkan maniyyata dole ne su bi ka’idojin kiwon lafiya tare da bin dukkan matakan kariya don kiyaye lafiyarsu yayin gudanar da aikin Hajji.”
Comments 1