Hukumar gudanarwar kungiyar kwallon kafa ta Kogi United FC ta Lokoja ta raba gari da kocin kungiyar Folabi Ojekunle.
Hakan na kunshe ne a wata takarda mai dauke da kwanan watan 26 ga watan Yulin shekarar 2022 kuma shugaban kungiyar Honorabul Abdulmalik Isah ne ya fitar da ita.
Isah ya godewa Ojekunle bisa irin ayyukan da ya yi wa kungiyar tare da yi masa fatan alheri a cikin ayyukansa na gaba.
A halin yanzu, Mataimakin Koci Chidi Oji ne zai karbi ragamar aiki, gudanarwar kungiyar har sai an nada bwani sabon koci.
KARANTA WANNAN LABARIN: Majalisar Dattawa Ta Tabbatar Da Bello A Matsayin Shugaban Hukumar RMAFC
Mai horar da yan wasan dake tsaron gida, Koci Alao Olaniyi ne zai taimaka masa.
A wnai labarin kuma na daban.
Mai martaba Sarkin Kano, Dakta Aminu Ado Bayero, ya sabunta lasisin tuki a hukumar kiyaye afkuwar hadurra ta kasa (FRSC) da ke hukumar tattara haraji ta jihar Kano Kano, a Kano.
Sarkin ya samu lasisinsa na farko a shekarar 1982, kamar yadda wata sanarwa da aka fitar ranar Talatar nan ta bayyana.
Sanarwar ta fito ne daga bakin kwamandan hukumar FRSC reshen jihar Kano, CC Zubairu Mato, a Kano.
Sanarwar ta ce a ci gaba da ziyarar ban girma na Sarkin; akwai bukatar sarakunan gargajiya su kwadaitar da talakawansu wajen aiwatar da yi lasisi.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Hakanan ya nuna mahimmancin samun lasisin saboda yana iya zama katin sheda wato ID card na sirri.
Ya kuma ce ana iya amfani da shi don ayyuka da yawa na kasa da na wajibi a banki, don inshora, asibitoci don taimakawa wajen fayyace da’awar kan ka.
Sanarwar ta ce “ana iya musayar lasisin tuki na kasa tare da lasisin tukin kasashen waje”.
Tun da farko, Ado-Bayero ya ja hankalin jama’a da su rika tuka ababen hawa, babura mai kafa uku da aka fi sani da Keke Napep ko adaidaita sahu da babura da su yi musu lasisi tare da sabunta su idan wa’adinsu sun kare.
Ya kuma bukaci sauran shugabannin gargajiya da su nuna alamar shugabanci su fito da kansu domin sabunta lasisi.
Ya godewa babban kwamandan hukumar FRSC reshen jihar Kano, shugaban hukumar tara haraji ta jihar Kano (KIRS) da daraktan hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa bisa jajircewarsu wajen ganin an samar da muhallin ababen hawa cikin sauki da kwanciyar hankali a jihar.
(NAN)