Wata babbar kotu dake jihar Oyo ta umarci hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da ta biya Cif Sunday Adeyemo Wanda akafi sani da Sunday Igboho diyar naira biliyan 20.
Mai Shari’a Ladiran Akintola ne ya yanke wannan hukunci, bayan Kara da Cif Yomi Alliyu, lauyan dake kare Mai rajin kafa kasar Yarbawan ya shigar a gaban Babbar Kotun.
fari dai lauyan ya bukaci kotun da ta umarci hukumar DSS ta biya diyyar naira biliyan 500, sakamakon mamaye gidan Igboho da hukumar DSS din ta yi, a ranar 1 ga watan Yulin Shekarar nan, a garin Ibadan.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ana zargin Yan bindiga da kashe Lauya a jihar Imo
Kotun ta tabbatar da cewa, afkawa gidan Sunday Igboho da DSS ta yi Kai tsaye ta sabawa dokar.
Mai shari’a Ladiran ya soki DSS da yin aiki bisa abin da ya bayyana a matsayin “Zalunci da son zuciya” inji shi.
A wani labarin Kuma na daban.
Gwamnatin jihar Delta, a jiya, ta soke kwangilar miliyoyin naira don gina hanyar Asaba Oko-Amakom/Oko-Obiokpu/Oko-Anala da aka bayar a shekarar 2018 saboda rashin kyawun aiki.
Kwamishinan Yada Labarai na Jihar, Mista Charles Aniagwu, shine wanda yayi wa manema labarai karin haske a Asaba bayan kammala taron majalisar zartarwa ta jihar SEC, wanda Gwamna Ifeanyi Okowa ya jagoranta, ya ce hanyar da ta ratsa al’ummomin Oko a karamar hukumar Oshimili ta kudu ta jihar ta kasance babban kalubale, ga gwamnatin jihar tsawon shekaru, saboda yanayin yankin na musamman.
Aniagwu wanda shine Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamnan, Olisa Ifeajika, ya ce dan kwangilar ba ya aiki daidai da saurin da gwamnati ke tsammanin wanda ya sa dole aka soke aikin.
Da yake bayyana cewa an biya wasu kudade ga dan kwangilar a matsayin kudin hada kai, ya ce gwamnatin jihar za ta duba bayanan ta tare da tantance aikin kwangilar da nufin gano ko dan kwangilar zai maido wa gwamnati duk wani kudinta data bashi.
A wani labarin kuma Aniagwu ya ce gwamnatin jihar ta amince da ginawa da sake amfani da wani babban shirin ruwa a Okerenkoko a karamar hukumar Warri ta kudu a wani bangare na kokarin samar da ruwan sha da kuma rage cututtuka masu yaduwa.