Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta sanya ranar 18 ga watan Janairu da 20 ga watan Junairu shekarar 2022, a matsayin ranar da za a ci gaba da shari’ar shugaban haramtacciyar kungiyar fafutukar kafa kasar Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu, wanda ake tuhuma da laifin cin amanar kasa da ta’addanci.
Mai shari’a Binta Nyako, a ranar Alhamis, ta amince da bukatar a rage lokacin shari’ar.
A baya dai kotun ta sanya ranar 19 ga watan Janairu domin sauraren karar amma ta gayyaci bangarorin da ke da hannu a lamarin da su bayyana a ranar 2 ga watan Disamba domin baiwa kotun damar karbar wasu kararraki.
Sai dai Kanu bai halarci kotun ba domin sauraron karar.
Lauyan sa, Ifeanyi Ejiofor, ya bukaci a dage zaman sauraron karar a watan Disamba zuwa watan Janairu.
Sai dai Shuaib Labaran, wanda ya tsaya a matsayin lauyan gwamnatin tarayya, ya shaidawa kotun cewa cewa Yana adawa da wannan bukata.
Mai shari’a Nyako ta sanar da lauyan Kanu cewa ba za a yi la’akari da bukatar a rage lokaci ba saboda rashin isasshen lokacin shari’a a cikin littafin diary.
Daga nan ne kotun ta sanar da bangarorin cewa za ta mayar da dukkan shari’o’in da aka shirya yi daga ranar 18 zuwa 20 ga watan Janairu Mai zuwa, zuwa wasu ranaku domin samun damar gudanar da shari’ar Kanu kawai.
Alkalin ta umarci hukumar DSS da ta baiwa Kanu damar yin addininsa, canza tufafinsa kuma a ba shi damar samun kwanciyar hankali a wurin da ake tsare da shi.
Gwamnatin tarayya ta sake shigar da kara a kan Kanu, bayan an sake kama shi.
Laifukan sun shafi aikata laifukan cin amanar kasa da ta’addanci.