Alkali Inyang Ekwo na babbar kotun tarayya dake Abuja a ranar Laraba ya dakatar da daukar sabbin ‘yan sanda dubu goma (10,000) da hukumar ‘yan sanda ke kan yi.
Hukumar lura da jindadin ‘yan sanda wato Police Service Commission PSC ta shigar da karar Sufeto Janar da hukumar ‘yan sanda da ministan harkokin ‘yan sanda kotu kan shirin daukar sabbin ‘yan sanda ba tare da saninta ba.
PSC ta bukaci kotun ta haramtawa hukumar daukar sabbin mutane aiki saboda hakan ya sabawa kundin tsarin mulkin da ya kafa hukumar.
A makon da ya gabata, hukumar ‘yan sanda ta bayyana cewa za a saki sunayen wadanda suka samu nasara a atisayen daukar sabbin ‘yan sanda.