Wata babbar kotu tarayya ta dakatar da hukumar zabe mai zaman kanta takasa daga sanya wani shugaban hukuma a jihar Legas cikin shirin rabon kayan aikin zabe a jihar.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta tattaro cewa Mai shari’a Chukwujekwu Aneke na babbar kotun tarayya da ke zamanta a Legas ya dakatar da hukumar zabe ta kasa shiga aikin shugaban hukumar kula da gandun dajin Legas MC.
KU KARANTA KUMA Kotu Ta Dakatar Da DSS Daga Kama Shugaban Hukumar INEC
Musiliu Akinsanya, wanda aka fi sani da MC Oluomo, domin raba kayan zabe a jihar.
Kotun ta amince da rokon jam’iyyar Labour ta neman umarnin hana INEC amfani da MC Oluomo, wajen raba kayan aikin zabe a Legas. Kamar yadda jaridar Punch ta rawaito.
A Wani Labarin Kuma Dan Takarar Gwamnan Na NNPP Ya Yi Alkawarin Sabunta Birane Idan Aka Zabe Shi
Farfesa Oba Abdulraheem, dan takarar gwamnan jihar NNPP na jihar Kwara, ya ce zai fara aikin sabunta birane da ababen more rayuwa, idan aka zabe shi a matsayin gwamnan jihar.
Da yake magana kan ajandarsa ga al’ummar jihar Kwara a wata hira da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, Oba ya ce zai fara aikin gyara da kuma kula da manyan titunan birane da na karkara.