A yau Wata babbar kotun dake Zamanta a garin Minna Babban birnin jihar Niger, ta umarci Mohammed Barau Kontagora da ya daina ayyana kansa a matsayin Sarkin Sudan na 7 na Kontagora.
Umurnin ya biyo bayan sauraron karar da wasu masu Neman Kujeran guda 15 suka gabatar a gaban kotun.
Wadanda ake kara a cikin kudirin sun hada da sabon sarki, Mohammed Barau Kontagora, Babban Lauyan Jihar Niger, da Kwamishinan Kananan Hukumomi, Ci gaban Al’umma da Harkokin Masarautu na jihar.
Alkalin, Mai shari’a Abdullahi Mikailu ya hana wanda ake kara na farko, Mohammed Barau Kontagora, daga bayyana kansa a matsayin Sarki na 7 “har zuwa lokacin da za a saurari karar da mai shigar da kara ya nema”
KARANTA WANNAN LABARIN: Majalissar Dattawa ta Tabbatar da Mai Shari’a Hussein a Matsayin Babban Alkalin Abuja
“An ba da umurnin na wucin gadi kuma an hori duk wanda ake tuhuma, wakilinsu, ko wani mutum ta kowane sunan da ke aiki a kan hukuma ko mutanen da ke da’awar matsayin Sarkin Sudan na 7 na Kontagora har zuwa lokacin sauraro da tabbatar da kudirin masu shigar da kara, kan karar da aka shigar da a ranar 11/10/2022. ” inji Mai shari’an.
Tun kafin yanke hukuncin, Lauyan masu shigar da kara, W. Y. Mamman Esq, ya roki kotun da ta hana Barau gabatar da kansa a matsayin sarki na 7.
Kuma a karshe Kotun ta dage sauraran karar har izuwa ranar 20 ga watan Oktoba shekarar 2022.
Comments 1