Kotun daukaka kara da ke Calabar ta bayyana Mista Jarigbe Agom a matsayin zababben Sanata mai wakiltar yankin Cross Rivers ta Arewa.
Wani kwamitin da aka nada Mai dauke da alkalai uku, karkashin jagorancin Justis Chioma Nwosu-Iheme ne su ka bayyana hakan, a wani hukunci da Kotun ta yanke a yau Juma’a, a Calabar babban birnin jihar ta Cross Rivers.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kan Auren Mace Jagoran Yan bindiga a Katsina ya mutu
A hukuncin, kotun daukaka kara ta kori Sanata Stephen Odey, wanda ke wakiltar yankin Cross Rivers ta Arewa, a Majalisar dattijan Kasar nan
Kotun ta bayyana Jarigbe na jam’iyar adawa ta PDP, a matsayin dan takarar halattaccen a zaben Sanata na yankin, da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta gudanar tun ranar 5 ga Disamba, 2020.
Kazalika Kotun ta kuma soke satifiket din da INEC ta bai wa Sanata Odey , sannan kuma ta umarci Hukumar zaben ta kasa, da ta janye takaddar. Shaidar da ta bai wa Sanata Odey.
A wani labarin Kuma, na daban…..
Babbar Kotu a Jahar Akwa Ibom dake zamanta a Uyo Babban Birnin Jahar, a jiya ta yankewa wani Dan Shekara 27 Mai Suna Sylvester Emmanuel Ime hukuncin Kisa, sakamakon Fashi da Makami daya aikata.
Babban Jojin Kotun, Mai Shari’a Okon Okon shi ya yanke hukuncin Kisan, ga Dan Asalin Ekiti Itam a Karamar Hukumar Itu ta Jahar.
Kotu ta samu Ime dumu-dumu da aikata Fashi da Makami a wani Kamfani na Dam Dave dake kan hanyar Idoro, Uyo a ranar 18 ga watan Disamba na Shekarar 2016.
Kotun ta tsaya akan cewa Wanda aka zartar da Hukuncin a kansa, tare da wasu mutum biyar, sun farmaki Jami’an tsaro dake farfajiyar Kamfanin Dam Dave, tare da guduwa da motoci biyu da Naira Miliyan 7.
A jawabin shi na tabbatar da aikata laifin, ya gayawa Kotu cewa, wani Nonso ya kira shi a wayar tarho, daga Aba ta Jahar Abia, inda ya bukaci ya bashi bayanai akan Kamfanin, Wanda hakan ya bada nasarar Sata a Kamfanin.
Duk da sauran sun gudu, amma Jami’an tsaro na Farin Kaya na DSS sun bi ta hanyar wayar Ime, inda aka samu nasarar kama shi ta hanyar Budurwar sa wata Victoria.
Ime Wanda shine Uban tafiyar yace akwai sauran mambobin su da suka hada da; Eze da Auchi da Chibuzor dukkanin su daga Jahar Abia, Wanda har zuwa yanzu ba’a san inda suke ba.
A yanke hukuncin sa, Mai Shari’a Okon yace baza’a taba yin hakuri akan irin abubuwan bakin ciki da akeyi a Akwa Ibom, inda wasu daga waje suke daukar nauyin Fashi da Makami da Garkuwa da Mutane, satar kananan yara da sauran ayyukan ta’addanci, inda yace da yawa wadansu laifin ba’a jinsu a jahar, abune da baza’a kyale ga duk Wanda aka samu da hannu a ciki.”
Okon ya umarci a Kashe Sylvester Emmanuel Ime ta hanyar rataya.
Comments 1