Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Fatakwal, a ranar Alhamis, ta kori dan takarar gwamna na jam’iyyar APC a jihar Ribas, Tonye Cole.
Kotun ta soke takarar sa ne kan mallakar shaida zama dan kasa biyu, wato bayan Nigeria ya kuma samu shaidar zama ɗan wata kasar, inda aka ce Tonye Cole ɗan ƙasar Burtaniya ne.
KU KARANTA: Kotu Ta Tabbatar Binani A Matsayin Yar Takarar Gwamnan Adamawa
Kotun ta kuma ce APC ba ta bi dokar zabe da ta kawo Cole a matsayin dan takarar jam’iyyar ba.
Jam’iyyar PDP a jihar Ribas ta garzaya kotu don ta umurci hukumar zabe mai zaman kanta da kada ta amince da Tonye Cole a matsayin dan takarar gwamna na jam’iyyar APC bisa zargin zama dan kasa guda biyu kuma zaben delegate da ya samar da shi bai bi ka’ida ba saboda ba a yi shi bisa sanya idanun INEC ba.
Mai shari’a Emmanuel Obile a hukuncin da ya yanke ya amince da karar jam’iyyar PDP, cewa Tonye Cole bai cancanci tsayawa takarar gwamna ba.
Daga nan ya umurci INEC da ta cire sunan Tonye Cole daga cikin sunayen wadanda suka cancanci tsayawa takarar Gwamna a zaben 2023.
Hukuncin kotun dai ya sabawa hukuncin da ta yanke tun farko a kan karar da jam’iyyar APC ta shigar kan jam’iyyar PDP da kuma dan takararta na gwamna Siminialaye Fubara.
A cikin karar, Mai shari’a Obile ya yanke hukuncin cewa babu wata jam’iyya da ke da hurumin yin katsalandan cikin harkokin cikin gida na wasu jam’iyyun siyasa sannan kuma ya ce kotun ba ta da hurumin sauraron karar.
A wani labarin kuma: Sanatan Kano: Kotu Ta Soke Takarar Danburan Tare da Tabbatar Da Laila Buhari
Kotun daukaka kara a Kano ta soke takarar Sanata Danburam Nuhu da jam’iyyar PDP ta yi a matsayin dan takarar Sanata a Kano ta tsakiya.
A don haka ne, kotun ta amince da zaɓen fidda-gwani da jam’iyyar ta gudanar, ƙarƙashin shugabancin Shehu Wada Sagagi, wanda ya fitar da Laila Buhari a matsayin ƴar takara.
A ranar 26 ga watan Satumba ne wata babbar kotun tarayya da ke Kano ta yi watsi da karar saboda rashin hurumin shari’a, bisa hujjar cewa an shigar da karar ne a Kano maimakon Abuja, sabanin tsarin majalisar shari’a ta kasa NJC kan al’amuran da suka shafi kararraaki kafin zaɓe.