Daga: Abbas Yakubu Yaura
Wata babbar kotun jihar Filato da ke zamanta a Jos a ranar Juma’a ta sallami tsohon gwamnan jihar, Jonah Jang, tare da wanke shi daga laifukan almundahanar naira biliyan 6.3 da hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa take yi masa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ambaliyar Ruwa: Hukumar SEMA Ta Tabbatar Da Mutuwar Mutane Bakwai A Jihar Neja
Kotun da ke karkashin mai shari’a Christy Dabup ta kuma sallami wani tsohon mai karbar kudi a ofishin sakataren gwamnatin jihar Filato, Yusuf Pam, wanda aka zarge shi tare da tsohon gwamnan.
A wani labarin kuma, Yanzu-yanzu: An Kama Fitaccen Mawaki Ice Prince Zamani Kan Yunkurin Sace Jami’in Dan Sanda
Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta kama shahararren mawakin nan na Najeriya, Ice Prince, bisa laifin cin zarafin wani jami’in dan sanda.
An tattaro cewa da misalin karfe 3 na safiyar ranar Juma’a ne jami’an ‘yan sanda suka kama fitaccen mawakin nan Oleku crooer bisa laifin tuki ba tare da lacicin mota ba.