Daga: Abbas Yakubu Yaura
Mai shari’a Emeka Nwite na babbar kotun tarayya da ke Abuja, ya umarci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) da ta karba tare da buga sunan Godswill Akpabio, a matsayin dan takarar jam’iyyar APC na mazabar Akwa Ibom ta arewa maso yamma a zaben shekara mai zuwa na 2023.
KARANTA WANNAN LABARIN: Cikin Hotona: Peter Obi Ya Ziyarci Jonathan Gabanin Fara Yakin Neman Zabe
Da yake yanke hukunci, Mai shari’a Nwite ya bayyana cewa INEC ta aikata ba bisa ka’ida ba saboda ta ki karba da kuma buga sunan Akpabio ko da APC ta aike mata da shi a matsayin dan takararta.
A wani labarin kum, Gwamnatin Tarayya Ta Saki Wasu Da Ake Zargin Mambobin Kungiyar IPOB Ne Da Aka Kama
Gwamnatin tarayya ta saki wasu da ake zargin ‘yan kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra ne da jami’an sojojin Najeriya suka kama tun ranar 27 ga watan Fabrairun shekarar 2020 a unguwar Imo River dake jihar Abia.
Wadanda abin ya shafa, Sunday Nwafor, mai shekaru 59; Uzonwanne Ejiofor, 48; da Wilfred Dike, mai shekaru 36, an tsare su a birgidiya 14 ta sojojin Najeriya Ohafia,dake jihar Abia sama da shekaru biyu, kamar yadda jaridar PUNCH ta tabbatar.
A halin da ake ciki, Amnesty International a Najeriya, ta yi maraba da sakin mutanen uku.
A cikin wata sanarwa da ta fitar a daren Larabar da ta gabata, Amnesty International ta bukaci gwamnati da ta bayar da bayanai game da halin da sauran wadanda aka tilastawa bacewar da kuma tsare su ke ciki.