A ranar Litinin ne aka yankewa wani mai garkuwa da mutane, Chukwudumeme Onwuamadike, wanda aka fi sani da Evans, da wanda ake karansa, Victor Aduba, hukuncin daurin shekaru 21 a gidan yari. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito
Mai shari’a Oluwatoyin Taiwo na kotun hukunta manyan laifuka ta Ikeja da ke jihar Legas ne ya yanke hukuncin.
KARANTA WANNAN LABARIN: Babbar Kotu Ta Sanya Ranar Hukunci Kan Karar Gwamnatin Tarayya Da ASUU
Wadanda aka yanke wa hukuncin, an zarge su ne da hada baki da kuma yin garkuwa da Sylvanus Ahanonu Hafia a ranar 23 ga watan Yunin shwkarar 2014, a hanayar Kara Street dake yankjn Amuwo Odofin na Legas.
Ana zargin sun kama Hafia tare da tsare shi kuma sun nemi a biya su kudin fansan dayakai dalar Amurika Milliyan 2.
A WANI LABARIN KUMA: Yakin Ukriane- Rasha: Ukriane Ta Dawo Da Dakarunta Dake DR Congo
A dai dai lokacin da ake cigaba da yaki tsakanin Rasha da Ukraine, Sojojin Ukraine 250 dake tawagar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya dake aiki a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango sun koma gida don taimakawa kasar su wajen yakar sojojin Rasha.
BBC ta ruwaito cewa, A lokacin da aka sanar da janyewar sashen kula da zirga-zirgar jiragen sama na Ukraine a watan Maris, jami’an diflomasiyya sun yi gargadin cewa lamarin zai bar tawagar Majalisar Dinkin Duniya da karancin jirage masu saukar ungulu.