Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi watsi da karar da gwamnatin tarayya ta shigar na tasa keyar mataimakin kwamishinan ‘yan sanda Abba Kyari da aka dakatar zuwa kasar Amurka.
A hukuncin da ya yanke a ranar Litinin din nan, Mai shari’a Inyang Ekwo ya yi fatali da karar da Abubakar Malami, babban lauyan gwamnatin tarayya kuma ministan shari’a ya shigar, bisa hujjar cewa bukatar ba ta cika ba.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa an dakatar da Abba Kyari ne bisa zargin da ake masa na ta’ammali da hodar ibulis, da wasu manyan kudade da aka samu a asusunsa.