By Abbas Yakubu Yaura
Kotun Daukaka Kara ta Enugu a ranar Juma’a ta kori karar da ke neman a kori Gwamnan Ebonyi David Umahi da Mataimakinsa Kelechi Igwe daga ofis saboda sauya sheka.
DUBA WANNAN LABARIN: Gwamnatin Gombe Ta Kaddamar Da Manhajar Wayoyin Hannu Don Tallafawa Harkokin Kiwon Lafiya
Su biyun a watan Nuwambar shekarar 2020 sun sauya sheka zuwa jam’iyyar APC daga jam’iyyar PDP.
Bayan ficewarsu, dan takarar jam’iyyar APC a zaben gwamna na shekarar 2019, Sanata Sonni Ogbuoji da abokin takararsa, Justin Ogbodo Mbam, sun garzaya wata babbar kotun jihar Ebonyi suna neman ta kori gwamnan da mataimakinsa.
Masu shigar da kara sun roki kotun da ta bayyana kujerun Umahi da Igwe a matsayin wadanda ba su da tushe, saboda sauya sheka daga PDP zuwa APC.
Ogbuoji da Mbam sun kuma bukaci Kotun da ta bayar da umarnin a rantsar da su nan take a matsayin Gwamna da Mataimakinsa da suka zo na biyu a zaben da aka ce.
Amma babbar kotun da ta yanke hukunci a ranar 28 ga watan Fabrairu, ta yi watsi da karar tare da bayar da naira 500,000 a matsayin diyya ga wadanda suka shigar da karar.
Sai dai kuma ba su gamsu da hukuncin ba, masu gabatar da kara sun daukaka kara kan hukuncin.
Amma a cikin hukuncin na mintuna 37, Kotun daukaka kara ta amince da hukuncin da karamar Kotun ta yanke kan lamarin.
Alkalan daukaka kara, a cikin wani hukunci na bai daya da mai shari’a Alfa Belgore ya karanta, ta yi watsi da karar saboda sabawa kundin tsarin mulkin kasar da kuma sauran dokokin kasar.