Kotun Ƙolin tarayya ta tabbatar tare da jaddada nasarar gwamnan Jihar Ondo Rotimi Akeredelu.
Akeredelu ya lashe zaben gwamnan jihar ne a zaben gama gari da aka gudanar a shekara ta 2019.
A wani zaman hadin gwiwa da aka yi a ranar Laraba, Alkalin kotun mai Shari’a Emmanuel Agim da wasu sauran manyan masu Shari’a hudu sun sanya kafa sun shure karar da dan takarar PDP Eyitayo Jegede ya shigar ne.
Idan ba a manta ba dai Jegede da jam’iyyarsa ta PDP sun shigar karar ne a abinda suka kira rashin adalci yayin gudanar da zaben.