tambuwal

Yanzu-Yanzu: Kotun Koli Ta Tabbatar Da Nasarar Tambuwal A Matsayin Gwamnan Sakkwato

Rahotanni daga Kotun Koli ta kori karar Ahmed Aliyu na APC ta tabbatar wa Aminu Waziri Tambuwal na PDP da kujerarsa ta gwamnan Sakkwato.

Tunda farko dai a yau, an fara da shari’ar Kano ne ta Abba Gida-Gida da kuma Ganduje.

Wannan hukunci na yau Kotun Koli na nufin Abba Gida-Gida kamar yadda aka fi saninsa, ba zai iya kara daukaka kara ba.

Haka zalika shima Ahmed Aliyu na APC a Sakkwato ba zai iya daukaka kara ba.

Mai shari’a Sylvester Ngwuta ne ya jogaranci yanke hukuncin na Kano tare da sauran alkalan da suka hada da Mai shari’a Kudirat Kekekere-Ekun da Mai shari’a Olukayode Ariwoola da Mai shari’a Amina Augie da kuma Mai shari’a Uwani Abba-Aji.

Abba Kabir Yusuf ya fara kai kara kotun sauraron kararrakin zabe da ke zamanta a Kano a watan Afrilun 2019, inda bayan sauraron korafe-korafensa, kotun ta kori karar.

Daga baya ya mayar da karar gaban kotun daukaka kara wadda ita ma ta sake watsi da karar a watan Nuwamban 2019.

Sai kuma a yau Litinin 20 ga watan Janairun 2020, Kotun Koli ta yanke hukunci karshe wanda Abba ba zai sake samun wata dama ta kai kara ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *