Kungiyar manyan ma’aikatan jami’o’in Najeriya (SSANU) da kungiyar ma’aikatan da ba malamai ba ta NASU sun dakatar da yajin aikin da suke yi bayan wata ‘yar gajeruwar ganawa da ministan ilimi, Adamu Adamu a Abuja ranar Asabar din nan.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Ana sa ran dakatarwar za ta fara aiki daga ranar Laraba.
A cewar Ministan Ilimi, Gwamnatin Tarayya ta ware Naira Biliyan 50 don biyan alawus-alawus ga mambobin SSANU, NASU da kuma Kungiyar Malaman Jami’o’i.