Kakakin majalisar dokokin jihar Filato, Yakubu Sanda na jam’iyyar APC ya sha kaye a yunkurinsa na komawa zauren majalisar. Kamar yadda Channels TV ta ruwaito.
Dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Mrs Happiness Matthew Akawu, ta yi nasara a zaben da aka yi a ranar Asabar din da ta gabata na neman kujerar dan majalisar wakilai ta mazabar Pengana.
KARANTA WANNAN LABARIN: INEC ta wallafa Kaso 96 cikin 100 na sakamakon zaben gwamnan Ogun
Yar takarar PDP ta samu kuri’u 9,926 inda ta doke Shugaban Majalisar wanda ya samu kuri’u 7,936. Yayin da jam’iyyar PRP ta samu kuri’u 6,721, jam’iyyar Labour kuma ta samu kuri’u 1,028.
Gadai sakamakon zaben Pengana a kasa:
APC – 7,936
PDP – 9,926
PRP – 6,721
LP – 1,028
A wani labarin kuma, Zargin Sayen Kuri’a: Kwamishina A Bauchi Ya Nisanta Kansa Da Wani Faifain Bidiyo
Kwamishinan matasa da wasanni na jihar Bauchi, Alhaji Adamu Manu Soro, ya musanta cewa shi ne a cikin wani faifan bidiyo da aka yi zargin cewa yana sayen kuri’u ga jam’iyyar PDP mai mulki a jihar. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Bidiyon, wanda aka wallafa a shafin yanar gizon yanar na Twitter, ya fara yaduwa ne kafin zaben gwamnoni da na ‘yan majalisar dokoki da aka yi ranar Asabar a jihar.