Majalissar Dattijan a yau Talata ta amince da Kara Samar da Sabbin Makarantun horas da aikin Lauya a dukkannin yankunan kasar nan 6
Hakan ya biyo bayan rahoton da Shugaban Kwamitin majalissar Mai kula da harkokin Shari’a, Yancin Dan Adam, da kuma dangogin su, Sanata Opeyemi Bamidele na jam’iyar APC daga jihar Ekiti ya gabatar a zauren majalissar.
Yanzu haka Cibiyoyin horas da aikin Lauyan da ake da su a kasar nan sun hada da: ta jihar Legas dake yankin Kudu maso yamma, Abuja dake yankin Arewa ta Tsakiya, Kano dake yankin Arewa maso yammata, Enugu dake yankin Kudu maso Gabas, da Kuma na Yenegua dake Kudu maso Kudu.
Yanzu wadanda majalissar Dattijan ta amince a Samar sun hada da: Kabba Law School dake jihar Kogi a yankin Arewa ta Tsakiya, Maiduguri Law School Campus dake jihar Borno a yankin Arewa maso Gabas, Argungu Law School Campus, dake Kebbi a yankin Arewa maso yamma,
Kana sauran sun hada da; Okija Law School Campus, dake jihar Anambra a yankin Kudu maso Gabas, Orogun Law School Campus dake jihar Delta a yankin Kudu maso Kudu, Ilawe Law School Campus dake jihar Ekiti a yankin Kudu maso Yamma, da kuma Jos Law School Campus dake yankin Arewa ta Tsakiya.