By Abbas Yakubu Yaura
Bayan watanni shida ne dai rahotanni suka ce majalisar dokokin jihar Zamfara ta fara wani sabon yunkuri na tsige mataimakin gwamnan jihar mai ci Mahdi Aliyu Gusau.
‘Yan majalisar dokokin jihar dai a watan Yulin shekarar 2021, sun tuhumi mataimakin gwamnan na jam’iyyar PDP, tare da ba shi wa’adin sa’o’i 48 da ya gurfana a gabanta bisa zargin rashin da’a da aka yi masa.
Abin jira a gani shine hanyar da majalisar dokokin jihar za ta bi a wannan karon.
Comments 1