• Majalissar Dattijai ta sake amincewa da wani Kwamishina a Hukumar INEC
• Farfesa Sani Muhammad Adamu da ya fito daga Yankin Arewa ta Tsakiya, shine majalissar ta aamince da shi matsayin Babban Kwamishinan hukumar ta INEC.
• Kwamitin dake kula da harkokin hukumar INEC a majalissar dattijai ne ya wanke Farfesa Adam kafin majalissar ta amince da shi a yau.
Majalissar dattijai a yau Alhamis ta tabbatar da na da Farfesa Sani Muhammad Adamu da ya fito daga Yankin Arewa ta Tsakiya, a matsayin Babban Kwamishinan hukumar zabe Mai zaman kanta ta kasa INEC.
Hakan na zuwa ne, bayan gabatar da rahoton kwamitin dake kula da harkokin hukumar INEC na majalissar ya gabatar a gabanta.
A ranar Talatar da ta gabata ne dai, Majalisar ta ki amincince wa da Farfesa Adam a matsayin Babban Kwamishinan hukumar, inda a lokacin majalissar ta ce, ba’a gama wanke shi ba, daga zarge-zargin da ya dabai baye shi.
KARANTA WANNAN LABARIN:Daga cin Amala: Mutane uku sun bakunci lahira a Kwara
Shugaban kwamitin dake kula da harkokin hukumar zabe Mai zaman kanta ta kasa INEC, a majalissar dattijai, Sanata Kabiru Gaya na jam’iyar APC mai mulki ne, ya gabatar da da rahoton a yau Alhamis a zauran majalissar, inda ya ce, binciken da kwamitin ya gudanar a kan zarge-zargin da ake w aAdam, ya nuna cewa, bai da wani illa tattare da kimar shi.
Comments 1