Daga: Uzairu Lawan Rigasa
Wasu Jiga-Jigan Malamai takwas ne daga kungiyar addinin Vadzidzi VaJeso suka nutse jiya Asabar a kogin Mazowe da ke Kasar Rushinga, yayin da suke fafatawa domin nemo “sanda mai tsarki” a cikin ruwan Rafin mai zurfin gaske, lokacin da ake gudanar da ibadar zabar Wanda zai kasance Jagoran Kungiyar.
Shugaban kula da harkokin ci gaban lardin Mista Timothy Maregere ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai, inda kuma ya ce dukkannin wadan da suka mutun maza ne kuma an tsinto gawarwakin.
Kazalika ya ci gaba da cewar kungiyar Malaman ta kunshi “Waliyau” guda 10, Amma kuma biyu ne kadaii suka tsira da rayuwar su.