Daga Jaridar Dimokuraɗiyya
Gamayyar Malamai da Limamai da Alarammomi a jihar Bauchi sun gudanar da taron walima da saukar Al-Qur’ani mai Girma na fatan Nasara da sanya albarka ga takarar Yahaya Bello a zaɓen da ke tafe na shekarar 2023.
Taron na gudana ne a yinin yau Asabar, 5 ga watan Fabrairun shekarar 2022.
Wannan dai na zuwa ne kasa da sa’oi 24 da Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya amsa kiraye-kirayen yan Najeriya, da kuma Taron talakawar dake neman ya fito takarar shugabancin kasar nan a zaben shekarar 2023.
Gwamnan ya amsa kiran ne a lokacin da hadaddiyar kungiyar yan Jaridun Hausa suka gana dashi jiya Juma’a 4 ga watan Fabrairun shekarar nan, a Babban Birnin Tarayya Abuja, bayan ya yi sha’warwari da amintattunsa.
Al’uma da dama dai da suka hada da kungiyoyin Fararan Hula, Addinai, Matasa da dai sauran su, na goyon bayan tsayawa Takarar Yahaya Bello a matsayin Wanda zai maye gurbin Shugaban kasa Buhari a Babban zaben kasa mai zuwa a shekarar 2023.