Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami (SAN), bai yi murabus ba.
Mataimakin sa kan harkokin yada labarai, Umar Gwandu ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a daren yau Alhamis.
A cewar Gwandu, Malami ya jajirce wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansa da kundin tsarin mulkin kasar ya tanada kamar yadda wasu dokoki suka tanadar.
A baya dai jaridar PUNCH ta ruwaito cewa Malami, a ranar 17 ga Maris, 2022, ya ce ba zai yi murabus daga mukaminsa ba, yana mai cewa zai kare wa’adinsa a matsayinsa na minista.
“A zahiri akwai ƙarshen komai. Har yanzu zamana a ofis bai kare ba. Ina addu’a don kyakkyawan karshe,” in ji shi.
Malami mai shekaru 54, ya kasance fitaccen mamba a majalisar ministocin shugaban kasa,Muhammadu Buhari tun daga shekarar 2015.
An ce shugaban yana matukar girmama shi wanda rahotanni suka ce yana neman shawararsa ta fuskar shari’a kan manyan al’amuran kasa.
An kuma tabbatar da kallon kimar da Buhari ke yi wa Malami a shekarar da ta gabata lokacin da Shugaban kasar a wata hira da ya kasa yin kalaman da suka “ci karo da babban lauyan sa”.
A kwanakin baya an yi ta yayata cewa dan asalin jihar Kebbi yana da sha’awar maye gurbin Gwamna Abubakar Bagudu amma mai taimaka wa Malami (Gwandu), a wata sanarwa da ya fitar, ya ce har yanzu shugaban nasa bai bayyana sha’awar Neman kowane irin mukami a Babban zaben 2023 ba.