Manchester City ta cimma yarjejeniya kan daukar dan wasan gaban Norway Erling Haaland daga Borussia Dortmund.
Haaland, mai shekara 21, zai koma City a wannan bazarar bayan sun kulla yarjejeniyar biyan fan miliyan 63.2 na ragowar kwantiraginsa.
Yarjejeniyar ta kawo karshen farautar da kungiyar ke yi na neman wanda zai maye gurbin dan wasan da ya fi kowa zura kwallo a raga wato Sergio Aguero, wanda ya koma Barcelona kyauta a bazarar da ta wuce.
A wani labari Kuma na daban.
Mamakon Ruwan Sama Da Tsawa Sunyi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 5 Tare Da Jikkata 41 A Damaturu
Akalla mutane biyar ne aka tabbatar da mutuwarsu, yayin da wasu 41 suka samu raunuka daban-daban a ranar Litinin din da ta gabata, yanzu haka ana kwantar da su a Asibitin kwararru da ke Damaturu Jihar Yobe sakamakon mamakon ruwan sama da kuma tsawa.
Babban Sakataren Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Yobe (SEMA) Dokta Mohammed Goje ya tabbatar da faruwar lamarin ga wakilinmu a Damaturu a ranar Talata.
A cewar sa “SEMA ta mayar da martani ga wadanda ginin ya rufta saboda tsananin iska da ruwan sama da aka asamu”.
“Tawagar bincike da aikin ceto ta Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Yobe SEMA a ranar 9 ga watan Mayu, 2022 ta amsa kiran gaggawa daga al’umomin yankin da abin ya shafa.
Hukumar tace ta aike da tawagar jami’an ta don tallafawa wajen kwashe wadanda abin ya shafa zuwa asibitin kwararru na jihar Yobe.”
Goje ya bayyana cewa “jimillar wadanda abin ya shafa 41 sun fito ne daga al’ummomi/da yan kuna daban-daban guda 6.
A cewar sa yankunan sun hada, Waziri Ibrahim, unguwar Abbari, NayiNawa, Pompomari, Sai rukunin gidajen ‘yan majalissu, kan titin Gujba da kuma Maisandari.
Kazalika yace abin takaici mutane 5 sun mutu maza 2, mace babba 1, da kuma ‘yan mata guda 2.
Comments 1