Wasu masu amfani da layukan MTN a halin yanzu suna fuskantar ƙarancin Sabis, kuma suna kasa yin zumunci da ƴan uwa da abokanan arziki, da abokanan hulɗa a wasu sassan Nigeria.
Majiyar Jaridar Dimokuraɗiyya ta ruwaito cewar, wasu masu amfani layukan a halin yanzu sun kasa yin kira, da bude Data, da tura saƙonni da sauran su.
KARANTA WANNAN LABARIN: Za’a ƙara Kuɗaɗen da ake biyawa Lemu haraji a Shekarar 2022 — Cewar Ministar Kuɗi
“Emergency Calls only” shine abinda ke nunawa a mafiya yawan wayoyin masu amfani da layin, ya zuwa lokacin da ake haɗa Wannan rahoton da misalin ƙarfe 4:30 a ranar Asabar.
Masu amfani da layin Sun ce sun fara fuskantar matsalar da misalin ƙarfe 2:30 na ranar Asabar.
Da yawan waɗanda suka yiwa majiyar Jaridar Dimokuraɗiyya bayani sun ce, tuni sun koma amfani da wani layin domin cigaba da gudanar da harkokin rayuwarsu.
@kessyl ta rubuta a shafin ta “Babu sabis na MTN gaba ɗaya a Abuja… Mike faruwa ne?
Akwai wani da zai iya yiman bayani akan mike faruwa da MTN @AjibolaJibsin
Duk ƙokarin da akayi na ganin an tattauna da Manajan MTN Funso Aina bai yi samu ba.
Layin MTN shine yafi kowane layi mafiya yawan masu amfani dashi, inda suke da mutane miliyan 77.35