Jami’an Rundunar Yan sanda sun cafke wasu mutane uku da ke da hannu a sace dalibai sama da 100, na makarantar Bethel Baptist na jihar Kaduna.
Jami’an hulda da jama’a na rundunar, Frank Mba ne ya gabatar da wadanda ake zargin, wadanda kuma aka same su sanye da kakin soji, a Shelkwatar rundunar ta musamman da ke yaki da fashi da makami SARS, na Babban Birnin Tarayya a Abuja.
Ya Kuma bayyana sunayen Wadanda ake zargin kamar Haka; Adamu Bello, Isiaku Lawal da kuma Muazu Abubakar.
Ya yin da suke jawabi wadanda ake zargin sun bayyana wa manema labarai cewa, Su 25 ne suka kitsa Garkuwa da daliban Makarantar dake Kaduna.
KARANTA WANNAN LABARIN: PDP ta Bukaci Gwamnan Babban Bankin Nigeria da ya sauka daga Mukamin sa
Kazalika sun bayyana cewa,sun aikata garkuwa da Daliban ne, bisa tsananin bukatar kudi.
Daya daga cikin wadanda ake zargin Mai suna Abubakar, kuma mai shekaru 27 ya ce, “Mu ashirin da biyar ne muka gudanar da aikin. Mun yi garkuwa da dalibai 136 kuma na samu Naira 100,000 daga cikin kudaden da muka amsa amatsayin kudin fansa. ” inji shi.