Wata majiya ta bayyana cewa a halin yanzu wasu da ake zargin mayakan IS ne na yankin yammacin Afirka (ISWAP) suna kai farmaki a wani kauye mai nisa da ke kudancin jihar Borno.
Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun afkawa Shallangba kusa da Debiro a cikin karamar hukumar Hawul da ke jihar a cikin motocin yaki, inda suka yi ta harbe-harbe a lokacin da mutanen kauyen suka tsere cikin daji.
A cewar wani jami’in ‘Civilian Joint Task Force’ (CJTF) ‘yan ta’addan sun yi galaba a kan mafarautan yankin kuma a halin yanzu suna cikin kauyen.
A yammacin Lahadi ne mahara suka kai farmaki a kauyen Debiro da ke kan iyaka da kananan hukumomin Biu da Hawul na jihar Borno.