Akalla manoma shida ne wasu da ake zargin ‘yan kungiyar IS ne a lardin Yammacin Afirka (ISWAP) suka yi garkuwa da su.
An yi garkuwa da mutanen ne a karamar hukumar Mafa da ke jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya a ranar Laraba.
A cewar Zagazola Makama, kwararre a fannin yaki da tada kayar baya kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a tafkin Chadi, ya ce wadanda harin ya rutsa da su galibi ‘yan gudun hijira ne, sun yi batan dabo ne bayan sun je gonarsu da ke kauyen Bulagarji da ke da nisan kilomita guda daga garin Mafa.
‘Yan uwan wadanda abin ya shafa da suka tabbatar da faruwar lamarin, sun ce maharan sun far wa manoman ne da sanyin safiyar ranar Laraba.
EFCC tace Kotu ta yanke wa Dubban Masu Laifi data gabatar a cikin watanni masu yawa
Daya daga cikin ‘yan uwan da ya nemi a sakaya sunansa ya ce ISWAP na neman kudin fansa nera miliyan biyar kafin su sako wadanda abin ya shafa.