Kimanin mutane 6 ake kyautata cewa an harbe su har lahira, yayin da membobin Mazhabar Shi’a a Nigeria, IMN suka yi arangama da jami’an tsaro a kofar Gwarimpa kusa da Galadimawa na Babbar birnin tarayya Abuja a yau Talata.
Mambobin kungiyar ta IMN da aka fi sani da ‘yan shi’a suna zagaye ne,lokacin da jami’an tsaro na hadin gwiwa suka bude musu wuta.
Har ila yau, majiyar Jaridar Dimokuradiyya ta samu labarin cewa, jami’an tsaro sun harbe yan Shi’a guda biyu a kusa da wani sabon bankin da ke kan titin 3rd Avenue a Rukunin gidaje na Gwarimpa dake birnin Abuja.
Lamarin ya jefa tattakin Mabiya Mazhabar Shi’a cikin rudani, yayin da mutane ke ta tserewa domin tsira. Sakataren kungiyar ta IMN, Abdullahi Musa ya tabbatar da faruwar lamarin.
KARANTA WANNAN LABARIN :Yan bindiga sun yi garkuwa Da wani Soji a Legas
“Suna harbin mutane ne kawai. Yayin da nake magana da ku yanzu, an kashe mutane shida. Har ma sun tafi da wasu gawawwaki, ”kamar yadda ya shaida wa manema labarai.
Mabiya Darikar Shi’a sun fito ne a safiyar yau Talata don ci gaba da jerin gwanon su don tunawa da ranar arba’in na kisan Imam Hussein, jikan Annabi Muhammad S.AW.
Comments 1