Fasinjoji tara a cikin wata motar haya sun gamu da ajalin su da sanyin safiyar yau Talata bayan wani taho muga da ta yi da wata babbar mota a Benin, babban birnin jihar Edo.
Lamarin mai ban tsoro ya faru ne a kan titin Sapele da ke cike da cunkoson jama’a ta hanyar Ogbelaka da misalin karfe 7.30 na safen yau, lokacin da yawancin mazauna garin ke hanzarin zuwa aiki, ofisoshi da wuraren kasuwancin su.
Babbar motar da ke ɗauke da yashi, wanda Direban ta ya gaza samun birki, ba zato ba tsammani ta kutsa tayi taho mugama da motar hayan ne, wanda ake kira Tuke-Tuke, inda ta kashe fasinjoji 9 nan take,
An ajiye gawarwakin wadanda aka suka mutu a dakin ajiyan gawarwaki, yayin da aka garzaya da fasinjojin da suka jikkata zuwa Asibitin Kula da kiwon Lafiya ICU na Asibitin Kwararru dake dake Benin na jihar Edo.
KARANTA WANNAN LABARIN: NA gamu da matsalolin sosai, a harkar fim, cewar Masa’uda Yar Agadaz
Hatsarin ya haifar da cunkoson ababen hawa, lamarin da ya tilastawa mutanen dake yankin yin tattaki zuwa wuraren harkokin su na yau da kullun.
Kawo hada wannan rahoton majiyar Jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito cewa, Jami’an tsaro, da suka hada da yan sanda da mambobin kungiyoyin sakai, na kokarin Samar da dai-daito a inda hatsarin ya faru.
A wani labarin Kuma na daban.
Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya ce manufar hana kiwo a fili da wasu takwarorinsa na kudancin kasar nan suka dauka ba ta aiki a jihar sa, gwamnonin Enugu, Ribas, Akwa Ibom, Ondo da Legas duk sun sanya hannu kan dokar hana kiwo a sarari.
Wannan ya biyo bayan kudurin da aka cimma a taron Kungiyar Gwamnonin Kudu, inda gwamnonin kudancin suka tsayar da ranar 1 ga Satumba, 2021, a matsayin ranar da za a sanya hannu kan dokar.
A wata hira da yayi a gidan talabijin na Channels, Sule ya ce ya yi imanin shirin baya aiki, “Ba mu son manufar hana kiwo sa fili a yanzu, ba ta aiki,” in ji shi
Duk da haka, Sule ya ce ya yi imanin cewa rayuwar makiyaya ba ita ce hanyar da za a bi ba, “Abu daya da dukkan gwamnonin arewa suka yanke, mun ce hanyar da ake bi yanzu na kiwo a bude ta tsufa, ba ta da amfani, kuma ba za a iya dorewa ba,” in ji shi.
Ya kara da cewa a madadin dokar hana kiwo a fili, Nasarawa ta yanke shawarar amincewa da Tsarin Canjin Dabbobi na Kasa.Ya yi bayanin cewa gwamnatinsa ta yi shirin sasanta makiyaya ta hanyar kafa wuraren kiwo a wurare bakwai a cikin jihar, matakin daya dace an dauki shi tare da hadin gwiwar Ma’aikatar Aikin Gona ta Tarayya da Gwamnatin Netherlands.
“Hanya mafi kyau don yin hakan ita ce idan kuna da zaɓuɓɓuka don mutane, abu ne mai sauki Nasarawa tace cikin mako guda, za muje Majalisar don ci gaba da samun dokar hana kiwo.”
“To me zai faru da Fulanin da ke kai da kawowa? Idan Fulanin sun san dalilin da yasa baya aiki, hanya mafi kyau shine a basu wani abu mai aiki, ”inji shi.
Comments 1