Rahotanni sun ce mutane biyu mutu bayan sun kone kurmus a wata gobara da ta tashi a yankin Ohoro da ke karamar hukumar Ughelli ta Arewa a jihar Delta.
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne da sanyin safiyar ranar Alhamis, lamarin ya faru ne sakamakon fashewar wani abu da ya lalata gidaje sama da 30 da dukiyoyi na miliyoyin naira.
Rahotanni sun kuma bayyana cewa gobarar ta tashi ne a lokacin da wata babbar mota kirar granite ta kutsa cikin wata tanka mai Wanda hakanne yayi sanadiyar tashin gobarar.