Wani gini da ake ginawa ya ruguje a daya daga cikin kasuwannin sai da wayoyi wato GSM Market dake garin Kano na jihar Kano.
Ginin yana kan titin Beirut, wani yanki mai cike da jama’a a Kano.
Daily Trust ta ruwaito cewa, Ana fargabar mutane da dama sun makale a cikin baraguzan ginin.
A cewar wani ganau, wasu daga cikin mutanen da ke cikin ginin a lokacin da ya rutsa da su ba a iya ceto su ba saboda babu kayan aikin ceto.
KARANTA WANNAN LABARIN: Sojojin Najeriya Na Samun Nasarar Murkushe Yan bindiga, Yan ta’adda, Da Masu Garkuwa – Lai Mohammed
Ana iya jin muryar daya daga cikin wadanda suka makale a lokacin da aka kira shi a waya.
“Mun kira lambarsa ne kawai yana daukar waya. Sai dai babu yadda za a yi a tseratar da shi” a cewar daya daga cikin shaidun.
A halin da ake ciki, wani memba na tawagar ceto da ya isa wurin da lamarin ya faru, ya ce wani ma’aikacin su ya kai wurin domin karfafa kokarin ceto duk wadanda suka makale.
Wannan ci gaban dai ya zo ne kasa da mako guda da ruftawar wani gini da ke wani wuri mai cunkoson jama’a a Abuja, inda mutane biyu suka mutu.
A WABI LABBARIN KUMA: Babbar Kotun Tarayya Ta Ci Tarar EFCC Tarar Naira Milliyan 1
A ranar Talata ne wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta ci tarar naira miliyan daya ga hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC, sakamakon mamaye wani kamfani da ke Abuja ba bisa ka’ida ba. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
idan ba manta ba, Jami’an hukumar EFCC sun mamayewa Kamfanin mai suna, Fezel Nigeria Limited dake a fili mai lamba 792, Cadastral Zone Industrial Estate, Idu-Abuja, da karfi a farkon wannan shekarar ba tare da wani dalilin yin hakan ba.